Labarai

Zaben fidda gwanin APC: Tinubu na kan gaba da Ameachi, Osinbajo da tazara mai yawa

A halin yanzu dai tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ne ke jagorantar zabukan fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayin da ake cigaba da kidayar kuri’u.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, wakilin mu da ke sa ido a kan taron, ya ruwaito cewa Tinubu ya samu kuri’u sama da 1,000 yayin da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi ya zo da kuri’u 217.

Ku tuna cewa kimanin yan takara bakwai da suka hada da Gwamnan Jihar Ekiti, wanda ya kasance Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya janye daga takarar shugaban kasar inda ya jefa hular shi a bayan Asiwaju na Legas.

Ana sa ran babban taron jam’iyyar APC da ke gudana a dandalin Eagles Square da ke Abuja zai fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Masu Alaƙa