Labarai

Zaɓen fidda gwani na APC: Osinbajo ya ƙi janye wa Tinubu

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen da ke gudana.

Osinbajo ne na karshe a cikin mutane 22 da ke neman tsayawa takara da yayi jawabin shi a wajen babban taro na musamman da aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

“Ya ku wakilan mu, idan kuka kada kuri’a a daren yau, ku tabbatar da cewa kuri’un ku na dauke da addu’a, makomar ƴaƴan ku.

“Ba za ku iya yiwa kasar nan fatan alheri ba ku zabi wanda ba ku yi imani da shi ba.

“Halin da muke ciki ba zai sa shugaban kasa na gaba ya koyi aikin ba. Kuma zan kasance a shirye daga rana daya.

“A yayin aiwatar da ayyuka na a matsayin VP, an shirya ni don aikin da ke gaba kuma zan kasance a shirye daga rana ta farko.

“Don haka ne ni Osinbajo na gabatar da kaina gare ku, manyan wakilan mu, domin neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mu,” in ji mataimakin shugaban kasar.

Matakin da Osinbajo ya dauka na cigaba da tsayawa takara ya zo ne bayan wasu yan takara shida sun fice daga tseren na APC suka goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu.

Kafin jawabin na Osinbajo, an yi ta rade-radin cewa Osinbajo ma zai janye wa Tinubu.

Masu Alaƙa