Labarai

Zaɓen 2023: Jerin sunayen dukkan ƴan takarar shugaban ƙasa

Dukkanin jam’iyyun siyasa a Najeriya sun ware da zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Ranar 9 ga watan Yuni, 2022, ita ce wa’adin da hukumar zabe ta kasa, INEC, ta kayyade domin kammala zaben fidda gwani da kuma mika sunayen yan shugaban kasa.

Jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki ta zabi dan takararta a matsayin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar a dandalin Eagles Square, Abuja.

Tinubu ya doke babban abokin hamayyar shi kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika masa tutar jam’iyyar.

Babbar jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party PDP, makwanni guda kafin nan, ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa.

Ita ma jam’iyyar Labour, LP, tana da tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Peter Obi, a matsayin dan takararta.

Wannan shi ne jerin sunayen dukkan yan takarar shugaban kasa a kasar zuwa yanzu bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa:

  • Prince Malik Ado-Ibrahim (YPP)
  • Rabiu Musa Kwankwaso (NNPP)
  • Omoyele Sowore (AAC)
  • Peter Obi (LP)Prince Adewole Adebayo (SDP)
  • Kola Abiola (PRP)
  • Asiwaju Bola Tinubu (APC)
  • Atiku Abubakar (PDP)

Masu Alaƙa