Yara 35 Sun Mutu A Yankin Afar Na Habasha Da Ke Fama Fari Da Rikici

Akalla yara 35 ne suka mutu a cikin yan makonnin nan sakamakon fari da rikici a yankin Afar da ke arewa maso gabashin Habasha, a cewar wani asibiti a yankin da kungiyar likitocin agaji ta Doctors Without Borders.
Sanarwar da aka fitar jiya Alhamis ta zo ne kwanaki bayan da wani ministan gwamnati ya musanta cewa mutane sun mutu sakamakon karancin abinci.
“Yara 35 ne suka mutu a cikin makonni takwas da suka gabata kadai kuma fiye da kashi biyu bisa uku na wadanda suka kamu da cutar sun mutu a cikin sa’o’i 48 da aka kwantar da su,” in ji kungiyar Doctors Without Borders a cikin wata sanarwa da ta yi nuni da barkewar rikici a yankin da aka fi fama da shi.
Kasar Habasha na fuskantar matsalar fari mafi muni a cikin shekaru 40 da suka gabata, biyo bayan rashin samun ruwan sama a jere a yankin kahon Afrika. Yankin Afar ya kuma ga wasu munanan fada a yakin da ya barke a yankin Tigray mai makwabtaka da Habasha a watan Nuwamban 2020.
Hussein Adem, darektan asibitin Dubti da ke Afar, mafi girma a yankin kuma yana yiwa mutane sama da miliyan 1 hidima, ya tabbatar da mutuwar yaran ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press, ya kuma ce mutanen da ke kwarara cikin asibitin sun fito ne daga yankunan da ake rikici da juna da ke kan iyaka da Tigray.