Siyasa

Ya Kamata Ƴan Najeriya Su Gode Wa Allah Da Ya Kawo Buhari – Chukwuemeka Ezeife,

A wata hira da aka yi da shi kwanan nan, tsohon gwamnan jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su gode wa Allah da yasa shugaba Buhari ya mulki kasar.

Ezeife ya kara da cewa, da Allah bai sa hakan ta faru ba, da ‘yan Najeriya ba za su samu hadin kai ba domin a yanzu sun riga sun shiga zaben shugaban kasa na 2023. Ya cigaba da cewa, duk da cewa yana cikin masu sukar Shugaban kasa, amma a yanzu ya gane cewa Allah ne yasa ya zama shugaban kasa tun farko.

Yace: “Allah ya ba mu Buhari, kuma mu yiwa Buhari godiya. Idan Buhari bai zo ba, da ba mu kasance da haɗin kai kamar yadda muke a yanzu don neman 2023 ba. Don haka na gode wa Allah da ya kawo Buhari. Ina zargin Buhari, amma yanzu na gane cewa aikin Allah ne. Nufin Allah ne, domin ya nuna tsarin shi ga Najeriya.”

Da yake magana game da zaben shugaban kasa na 2023, Ezeife yayi kira ga INEC da ta samar da injina don hana magudin zabe, domin hakan na iya jefa kasar cikin rikici idan har aka bari hakan ya faru.

Madogara: The Sun News

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi