Siyasa

Wata Jam’iyya Na Shirin Ɗauko Mutane Haya Don Kamfen Shugaban Ƙasa A Kano – Buba Galadima

Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima ya koka kan wani shiri da ake zargin daya daga cikin jam’iyyun siyasa na shirin yi na hayar jama’a gabanin kaddamar da yakin neman zaben su na shugaban kasa a Kano ranar Talata.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi kwanan nan, Jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, Buba Galadima yace shirin da ake zargin jam’iyyar na yi shi ne don haifar da tunanin cewa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, Rabiu Kwankwaso ba shi ne dan takarar shugaban kasa kadai ba da ya shahara a Kano ba.

Abin da Galadina yace, “Na samu labarin cewa wata jam’iyya za ta je Kano domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a ranar Talata, kuma tuni suka yi jigilar Naira miliyan ₦500 don rabawa a fadin kasar nan domin su tara jama’a su nuna cewa ba Kwankwaso kadai ke da farin jini ba a Kano, mun ja musu kunne cewa ba za su taba samun kashi daya bisa dari na yawan jama’ar da Kwankwaso zai tara ba”.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi