Al'umma

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Yayi Tafiya Cikin Ruwa Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Garin Shi, Otuoke

A yau ne tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci yankunan Otuoke da wasu al’umomin jihar Bayelsa da ambaliyar ta shafa.

Ya bayyana hakan ne yau a shafin shi na Facebook da aka tabbatar. Rubutun ya haifar da martani da yawa daga magoya bayan shi da yawa a dandalin sada zumuntar.

Tsohon shugaban kasar wanda ya shiga cikin ruwa yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye garin shi da sauran al’ummomi ya bukaci dukkan ‘yan kasar da ke da hannu wajen nuna goyon baya ga wadanda abin ya shafa tare da bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Ambaliyar ruwa da ta afku a wasu jihohin kasar nan ya kasance babban abin damuwa ga wasu masu fada a ji a Najeriya. Tuni dai wasu ‘yan takarar shugaban kasa da suka hada da Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour suka ziyarci yankunan da lamarin ya shafa.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi