Ilimi

Tsarin Jami’o’in Najeriya Zai Ruguje In Babu ASUU – Osodeke

A ranar Lahadi ne shugabannin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) suka yi tir da halin rashin kulawa da gwamnatin Najeriya ke nunawa jami’o’in gwamnati a kasar.

A ranar Juma’a ne kungiyar kwadagon ta dakatar da yajin aikin da ta shafe watanni 8 tana yi, biyo bayan umarnin da kotun masana’antu ta kasa ta bayar.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, wanda ya bayyana hakan a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, Sunday Politics, ya dora alhakin ayyukan masana’antar a kan rashin gaskiyar gwamnati na mutunta yarjejeniyoyin da suka kulla da kungiyar.

Osodeke ya dage cewa kungiyar na da muhimmanci ga cigaban jami’o’in gwamnati a kasar.

Ya kuma kalubalanci gwamnati da ta ba da fifiko wajen bayar da kudade a jami’o’in gwamnati domin amfanin ‘yan Najeriya.

Yace: “A cire ASUU a yau, an iya gaya muku nan da shekaru biyu masu zuwa jami’o’in mu zasu zama kamar makarantun mu na firamare da sakandare. Kungiyar ta yi gwagwarmaya sosai don tabbatar da dorewar tsarin. Bai kamata a kalli kungiyar a matsayin matsala ba. Baya ga ganawar da ‘yan majalisar wakilai, babu wani jami’in gwamnati da ya kira mu don yin taro.

“Muna ba da ilimi fifiko. Yakamata a ware kashi cikin hankali bisa ga tsarin a cikin kasafin kudi. Yaranmu za a karfafa su su zauna a nan maimakon kashe makudan kudade zuwa kasashen waje. Daliban Najeriya sun cancanci a girmama su. Kada a nisantar da su daga makarantu ba dole ba.”

Osodeke ya kuma caccaki Ministan Kwadago da Aiki, Chris Ngige, kan yadda ya yi wa jama’a bayanin yajin aikin.

Ya kara da cewa: “Lamiri ne yasa ministan ya damu. ASUU ba ta da siyasa. Muna fafutukar ne domin biyan bukatar ‘yan Najeriya. Ministan ya je wajen jama’a ya yi karya.”

Rubuta Sharhi