Siyasa

Tinubu Ya Sani Cewa Jam’iyya Ta Ita Ce Najeriya – Inji Sanusi Lamiɗo

Tsohon Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya shaida wa mai rike da tutar jam’iyyar All Progressive Congress APC a zaɓen 2023 cewa ba shi da wata jam’iyyar siyasa.

A lokacin da yake jawabi a matsayin babban mai jawabi a karo na bakwai na KadInvest, taron da hukumar kula da zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya a Kaduna, tsohon gwamnan na CBN yace, “Ina ta maimaitawa, da fatan ku tuna cewa na rasa aiki na a babban bankin saboda haka, matsala iri daya. Ba wata jam’iyya ba ce, ba ni da jam’iyya, jam’iyya ta ita ce Najeriya, wannan ita ce matsalar da muka samu a 2014. Asiwaju (Tinubu) ya san jam’iyya ta ce Najeriya.

Da yake nasa jawabin, Sanusi yayi tsokaci kan batutuwa da dama da suka hada da batun kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), inda ya bayyana cewa kamata yayi a tafiyar da kamfanin a matsayin kamfani mai zaman kansa tare da bin diddigi. Ya kuma ce ya kamata jihohin Najeriya su daina dogaro ga gwamnatin tarayya fiye da kima.

Source: Gidan Talabijin na Channels.

Credit Photo: Google.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi