Labarai

Tinubu ya caccaki PDP bayan lashen fidda gwanin APC na shugaban ƙasa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki a 2023, Bola Ahmed Tinubu ya nuna fushin shi ga masu yiwa jam’iyyar APC fatan mutuwa.

Da yake jawabi yayin jawabin bayan nasarar lashe zaɓen fidda gwani a ranar Laraba, tsohon gwamnan jihar Legas ya zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP da yunkurin ruguza APC.

Yace babbar jam’iyyar adawa ta barnata shekaru 16 a kasar a lokacin da take mulki.

Yace, “Kun kunyata wadanda suka rigaya sun saya wa APC akwatin gawa, jam’iyyar mu tana nan da rai. Muna nan muna da kwarin gwiwa da jajircewa.

“Sun kira kan su PDP shekaru 16 na wahala da gazawa muka ce a koma gefe. Muna da karfin gwiwa cewa wannan al’ummar ta dawo kan turba”, inji Tinubu.

Masu Alaƙa