Syria Ta Dakatar Da Tashin Jiragen Sama A Damascus Bayan Da Isra’ila Ta Kai Hari

Kasar Syria ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da kuma tashi daga filin jirgin saman Damascus bayan wani harin da Isra’ila ta kai ranar Juma’a a wani yanki da ke kusa da filin jirgin, kamar yadda wata jarida mai goyon bayan gwamnati ta ruwaito.
Al-Watan ta ce harin ya bar titin jirgin a lalace, ba tare da bayar da karin bayani kan harin ba.
Filin jirgin saman yana kudancin Damascus babban birnin kasar inda masu fafutukar yan adawar Syria suka ce mayakan sa-kai da Iran ke marawa baya suna kai farmaki kuma suna da ma’ajiyar makamai. Isra’ila ta kwashe shekaru tana kai hare-hare a yankin, ciki har da wanda ya faru a ranar 21 ga watan Mayu wanda ya haddasa gobara a kusa da filin jirgin, lamarin da ya kai ga dage tashin jirage biyu.
Kamfanin dillancin labarai na SANA yace ma’aikatar sufuri ta tabbatar da cewa an dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama saboda “wasu na’urorin fasaha sun daina aiki a filin jirgin.” Bai ambaci harin ba.
Kamfanonin jiragen sama na Sham Wings masu zaman kansu sun ce yana karkatar da dukkan jiragen shi daga Damascus zuwa filin jirgin saman Aleppo da ke arewacin kasar. Ya kara da cewa duk fasinjojin za a yi jigilar su ta motocin safa a tsakanin garuruwan biyu kyauta.
Filin jirgin saman yana kudu da Damascus. Flightradar24 bai nuna tashin jirage a kusa da filin jirgin ba a ranar Juma’a da tsakar rana.
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria da ke da hedkwata a Birtaniya, mai sa ido kan yakin yan adawa, ta ce harin da Isra’ila ta kai da safiyar Juma’a, ta kai hari a ma’ajiyar makamai guda uku na mayakan sa-kai da Iran ke marawa baya a cikin filin jirgin, inda ta kara da cewa titin jirgin sama na arewa da ke wurin ya lalace kamar yadda hasumiya ta gani.