Labarai

Sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa 13 na APC da suka cancanta da 10 da ba su cancanta ba

An bayyana sunayen yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC 13 da kwamitin CheifJohn Oyegun ya ba da shawarar cewa sun cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa na babban zaben 2023.

Hakan kuma kwamitin ya ƙara bayyana wasu ƴan takarar shugaban ƙasa 10 a APC cewa ba su cancanta da tsayawa takarar ba.

Jerin sunayen ƴan takarar da suka cancanta:

 • 1. Bola Ahmed Tinubu
 • 2. Yemi Osinbajo
 • 3. Rotimi Amaechi
 • 4. Ahmed Lawan
 • 5.Yahaya Bello
 • 6. Kayode Fayemi
 • 7. Emeka Nwajiuba
 • 8. Ogbonnaya Onu
 • 9. Ibikunle Amosun
 • 10. David Umahi
 • 11. Badaru
 • 12. Godswill Akpabio
 • 13. Mr Tein Jack-Rich

Ƴan takarar da ba su cancanta ba:

 • 1. Tunde Bakare
 • 2.Rochas Okorocha
 • 3.Ben Ayade
 • 4.Sani Yerima
 • 5.Ken Nnamani.
 • 6.Ikeobasi Mokelu
 • 7.Demeji Bankole
 • 8.Felix Nicholas
 • 9.Uju Ken-Ohanenye.
 • 10. Robert Borroffice

A yau ne kuma ake sa ran yan takarar da aka wanke, suka cancanta za su karbi takardar shaidar kammala tantancewar su.

Masu Alaƙa