Sojojin Najeriya Na Aiki Da Boko Haram Da Ƴan Bindiga – Hafsan Sojan Najeriya, Irabor

A ranar 4 ga Afrilu, 2022, Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya (CDS), Janar Leo Irabor ya yi Allah wadai da karuwar shari’o’in da ake samu na jami’an soji da ke taimaka wa yan ta’adda, yan fashi, masu kisa, da sauran masu aikata laifuka a kasar.
Irabor, a cikin wata wasika da ya aikewa dukkan kwamandojin ayyuka daban-daban, wacce SaharaReporters ta samu ta musamman, ya bukaci su wayar da kan jami’an su dangane haɗarin hada kai da makiya.
Ya bayar da misali da wasu al’amura da dama na sojoji da aka kama dangane da ayyukan Boko Haram da sauran yan ta’adda, ciki har da kama wani soja da ya hada baki da wani sanannen dan ta’adda Babagana Kura a Bama, Borno.
“Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a cikin matakai daban-daban sun nuna karuwar lokuta na taimako da tallafi daga ma’aikata. Wannan cigaban ya fito ne a cikin rahotanni daban-daban na kama jami’an soji cikin kankanin lokaci,” inji wasikar da wani CE Oji ya sanya wa hannu a madadin CDS.
“Idan za a iya tunawa, wata kungiya ta kama wani soja da laifin hada baki da wani dan ta’adda da aka tabbatar da sunan shi Babagana Kura a karamar hukumar Bama, jihar Borno.
“Kame wadannan ma’aikatan na nuni ne da aiwatar da ayyukan cikin gida da ke cigaba da taimakawa abokan gaba, tare da yin tasiri nan take ko kuma mai yuwuwa kan ayyukan.”
A ranar Talata ne Shugaban Cocin Methodist ta Najeriya, Samuel Uche a lokacin da yake ba da labarin yadda ya kusa mutuwa a hannun masu garkuwa da mutane yayi zargin cewa wasu sojoji daga Arewa na aiki da masu garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Gabas.