Ƙetare

Sojoji 10 Sun Mutu, Kusan 50 Sun Jikkata A Harin Da Aka Kai Sansanin Sojojin Burkina Faso

Akalla sojoji 10 ne suka mutu yayin da wasu kusan 50 suka samu raunuka lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai hari a wani sansanin soji da ke yankin Sahel na kasar Burkina Faso a ranar Litinin din da ta gabata, in ji rundunar.

An kai harin ne kan runduna ta 14 ta Inter-Arms a Djibo.

Wani kiyasi na wucin gadi ya nuna cewa sojoji 10 ne suka mutu a fadan sannan an kwashe kusan 50 da suka samu raunuka zuwa cibiyoyin kiwon lafiya, in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

“Sojojin sun yi jajircewa wajen mayar da martani ga harbin kai tsaye daga makiya. Sun zo da adadi mai yawa, “in ji ta, inda aka kashe ‘yan ta’adda 18 yayin ayyukan da suka biyo baya.

Rundunar ta ce an tura jiragen yakin sama a yankin domin tabbatar da ceto da kuma kai dauki.

Burkina Faso dai ta sha fama da matsalar rashin tsaro a kai a kai sakamakon rikicin da ya barke daga makwabciyar ta Mali cikin shekaru goma da suka gabata.

A watan da ya gabata ne dai sojojin karkashin jagorancin Kaftin Ibrahim Traore suka kori Laftanar Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba wanda ya kwace mulki a watan Janairu. A makon jiya ne aka rantsar da Traore a matsayin shugaban rikon kwarya. ;

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi