Ƙetare

Shugabannin EU Sun Taya Giorgia Meloni Murnar Zama Firaministan Italiya

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen a ranar Asabar din nan ta taya shugabar mai ra’ayin mazan jiya Giorgia Meloni murnar zama firaministan Italiya, ta kuma ce tana fatan “hadin gwiwa mai ma’ana” da gwamnatin ta.

“Ina taya Giorgia Meloni murnar nadinta a matsayin Firayim Minista na Italiya, mace ta farko da ta rike mukamin,” von der Leyen ta wallafa a shafin shi na Twitter.

“Ina fatan kuma samun ingantacciyar hadin gwiwa da sabuwar gwamnati kan kalubalen da muke fuskanta tare.”

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel, shi ma yayi maraba da Meloni a matsayin sabon firaministan Italiya, ya kuma rubuta a shafinsa na Twitter cewa: “Bari mu yi aiki tare don amfanin Italiya da EU.”

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi