Siyasa

Shugabannin Ƙungiyar Goyon Bayan PDP Sun Koma APC A Sokoto

Shugabannin kungiyar magoya bayan jam’iyyar PDP a Sokoto sun koma jam’iyyar APC a jihar.

Bashar Abubakar, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga tsohon gwamna Aliyu Wamakko, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Sokoto.

Yace wadanda suka sauya sheka wadanda shugabannin wata kungiya ce mai suna “Ubandoma/Sagir Youth Mobilisation and Awareness Support Group,” sun samu tarba daga gwamnan jam’iyyar a jihar, Alhaji Ahmad Aliyu zuwa APC.

Abubakar yace: “Wadanda APC ta karba su ne Lukman Kwaire da Anas Muhammad, Shugaban kungiyar da Sakataren kungiyar.

“Masu sauya shekar sun kasance suna yiwa PDP aiki a fagage da dama amma basu samu akidar siyasa ba kuma sun maida hankali a cikin jam’iyyar wanda hakan yasa suka daina goyon bayansu suka koma APC.

“Sabbin mambobin sun fice daga PDP ne biyo bayan tsoma bakin daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Umaru Tambuwal.”

Masu Alaƙa