Shugaban Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi ya fice daga APC zuwa PDP
Sanata Yahaya Abdullahi, shugaban majalisar dattawa, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party PDP a jihar Kebbi.
Mai baiwa Abdullahi shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Jamil Gulma ya tabbatar da sauya shekar a ranar Talata.
Shugaban majalisar dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce zuwa karamar hukumar Kamba domin shelanta jam’iyyar PDP da kuma nuna sha’awar shi ta tsayawa takara,” kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito Gulma yana cewa.
Yahaya ya halarci zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC, inda aka ce bai samu kuri’u ba.
Tun daga nan ya yi watsi da sakamakon kuma ya kwatanta shi a matsayin abin shambolic da wasan yara.
An tattaro cewa mai yiwuwa sauya shekar tasa ba ta rasa nasaba da zaben fidda gwani na takarar gwamna da kuma wasu da dama da shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka kasa yi.