SERAP Ta Buƙaci Buhari Ya Gaggauta Dawowa Da Biliyan ₦1.4 na Fallafin Motoci Da Ya Bai Wa Ƙasar Nijar

SERAP ta cewa Buhari ya nemi Jamhuriyyar Nijar da ta dawo da tallafin motocin Naira Biliyan ₦1.4 kuma a gaggauta yin amfani da su momin biyan malaman ASUU.
Kungiyar SERAP ta bukaci gwamnatin Buhari da ta bukaci hukumomin jamhuriyar su dawo Nijar biliyan N1.4, sannan ta yi amfani da kudaden da aka dawo da su wajen kara kudaden da kungiyar ASUU take buƙata.
Gwamnatin Najeriya a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta, ta tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sayo tare da bayar da gudummawar motocin da kudin su ya kai Naira biliyan 1.4 ga makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar.
Wannan tonon silili ya tayar da jijiyar wuya kuma ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta ce tallafin na taimakawa Nijar ne domin magance matsalolin tsaro.
Da take mayar da martani, wata kungiyar farar hula mai suna SERAP ta wallafa a shafinta na twitter cewa: “Dole ne gwamnatin Buhari ta bukaci mahukuntan Jamhuriyar Nijar da su mayar da kudaden da suka kai Naira biliyan 1.4 da aka amince musu na sayen motoci, sannan su yi amfani da kudaden wajen karkatar da kudaden. ga ASUU, domin yaran talakawa su koma makaranta”.