Labarai

Sarkin Daura Mai Shekaru 91, Faruk Umar Ya Auri Budurwa Ƴar shekaru 22

Sarkin Daura mai shekaru 91 a duniya, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya auri wata yarinya ‘yar shekara 22 mai suna A’isha Yahuza Gona.

An yi daurin auren ne a garin Safana na jihar Katsina, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Majiyar da ta zantawa da Daily Trust, ta kuma bayyana cewa Sarkin da A’isha sun yi soyayya na tsawon mako guda a takaice kafin su daura aure a wani biki da ba’a gayyaci mutane sosai ba.

Ku tuna cewa a watan Disambar 2021, Sarkin ya auri Aisha Iro Maikano, ‘yar shekara 20.

Masu Alaƙa