Labarai

Sarki Salman Na Saudiyya Ya Nada Sabbin Manyan Jami’ai Da Jakadu

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ya nada sabbin shugabannin hukumomin tsaro da na bincike da jakadu a ranar Lahadi.

An nada Dr. Najm bin Abdullah al-Zaid a matsayin sabon mataimakin ministan shari’a da Ahmed bin Abdulaziz bin Ibrahim al-Issa a matsayin babban darakta na hukumar bincike.

Sabbin shugabannin da aka nada sun hada da Fahd bin Abdul Rahman bin Dahes al-Jalajel a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar abinci da magunguna; Khalid bin Muhammad bin Abdul Rahman al-Salem a matsayin Chariman na Royal Commission for Jubail da Yanbu a matsayin Minista; Badr bin Abdul Mohsen bin Abdullah bin Hadab a matsayin mataimakin shugaban kwamitin kwararru a majalisar ministocin kasar.

Bugu da kari, an nada Tariq bin Abdulaziz bin Abdul Rahman al-Faris a matsayin mai ba da shawara ga Sakatariyar Majalisar Ministoci, yayin da aka nada Dr. Abdul Rahman bin Abdullah bin Abdul Rahman al-Kanhal da Hammoud bin Badah al-Muraikhi masu bada shawara ga kotun masarauta.

Sabbin jakadun da aka naɗa sun hada da Adel bin Ahmed al-Jubeir a matsayin jakada mai kula da harkokin yanayi; Abdul Rahman bin Ahmed bin Hamdan al-Harbi a matsayin jakadan Saudiyya a Jamhuriyar Jama’ar Sin.

Sauran sabbin nade-naden sun hada da Manjo Janar Nayef bin Majid bin Saud Al Saud da aka kara masa girma zuwa mukamin Laftanar-Janar; Manjo Janar Muhammad bin Abdullah Al-Basami da aka kara masa girma zuwa mukamin Laftanar-Janar kuma aka nada shi Daraktan Tsaron Jama’a; da Abdul Rahman bin Suleiman Al-Siyari a matsayin dan majalisar Shura.

Masu Alaƙa