Labarai

Sanata Aishatu ta lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan Adamawa a APC

Wata yar majalisar dattawan Najeriya, Aishatu Binani ta zama wacce ta lashe zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress APC da aka gudanar a jihar Adamawa.

Aishatu Binani ta doke yan takara shida masu karfi da kwarewa wadanda suka hada da; Tsohon Gwamna; Jibrilla Bindow, Tsohon Shugaban Hukumar EFCC; Nuhu Ribadu, dan majalisar wakilai mai ci; Hon. Abdulrazak Namdas, Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar; Hon. Wafarniyi Theman, da babban dan kasuwa Mustapha Umar.

Sakamakon karshe na zaben fidda gwanin ya nuna kuri’a da kowane dan takara ya samu kamar haka; Wafari Themann – 21, Umar Mustapha (Otumba) – 39, Hon. Abdulrazak Namdas – 94, H.E Sen. Bindow Jibrilla – 103, Mal. Nuhu Ribadu – 288, da Sen. Aishatu Dahiru Binani – 430.

Masu Alaƙa