Labarai

‘Sabon Yaƙin Ruwan Sanyi’: Rasha Da Turai Na Neman Tasiri A Afirka

Afrika

Shugabannin kasashen Rasha da Faransa da kuma Amurka suna kai komo a nahiyar Afirka domin samun goyon bayan su ga matsayar su kan yakin Ukraine, lamarin da wasu ke cewa shi ne gasa mafi zafi na yin tasiri a nahiyar tun bayan yakin cacar baka.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da shugaban Faransa Emmanuel Macron kowannen su na ziyartar kasashen Afirka da dama a wannan mako. Samantha Power, shugabar hukumar raya kasashe ta Amurka, ta je Kenya da Somaliya a makon da ya gabata. Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, za ta je Ghana da Uganda mako mai zuwa.

“Kamar wani sabon yakin cacar baki ne ke gudana a Afirka, inda bangarorin da ke hamayya da juna ke kokarin samun tasiri,” in ji William Gumede, darektan ayyukan dimokuradiyya, wata gidauniya da ke inganta shugabanci nagari.

Lavrov, a cikin tafiye-tafiyen da ya ke yi a nahiyar da kasashe da dama ke fama da fari da yunwa, ya nemi ya bayyana kasashen yammacin duniya a matsayin miyagu, yana mai dora su kan tashin farashin kayan masarufi, yayin da shugabannin kasashen yammacin turai suka zargi fadar Kremlin da sakaci da amfani da abinci a matsayin makami. yaƙe-yaƙe na cin nasara irin na sarakuna – kalmomi da aka lissafta don jan hankalin masu sauraro a Afirka bayan mulkin mallaka.

Masu Alaƙa