Rikicin Kabilanci A Yankin Darfur Na Kasar Sudan Ya Laƙume Rayuka 100

Rikicin kabilanci a cikin makon da ya gabata a yankin Darfur na Sudan yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100, hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da wani dattijon sun fada jiya litinin, a tashin hankali na baya bayan nan a yankin da ke fama da rikici.
Toby Harward, jami’in hukumar kula da yan gudun hijira ta UNHCR, yace fadan ya samo asali ne sakamakon rikicin kabilanci tsakanin kabilun Larabawa da na Afirka a garin Kulbus da ke lardin yammacin Darfur. Daga nan ne mayakan Larabawa na yankin suka kai hari a kauyuka da dama a yankin, lamarin da ya tilastawa dubban mutane tserewa, in ji shi.
Abkar al-Toum, shugaban wata kabila a garin, yace wadanda suka mutu sun hada da akalla gawarwaki 62 da aka gano sun kone bayan da mayakan sa kai sun kona kauyuka fiye da 20. Yace mutane da dama har yanzu ba’a gan su ba. Yayi ikirarin cewa maharan sun samu iko da albarkatun ruwa, lamarin da ya kara ta’azzara halin jin kai a yankin. Sai dai bai yi karin haske ba.
Abbas Mustafa, wani jami’in yankin yace hukumomi sun tura karin dakaru zuwa yankin. Yace a satin da ya gabata fadan ya raba da su muhallan su akalla iyalai 5,000.
Harward yayi kira ga “dakarun hadin gwiwa masu tsaka-tsaki” don ba da kariya ga fararen hula a yankin. “Idan ba a shiga tsakani ko sasantawa ba, kuma aka bar tashin hankali ya cigaba, manoma ba za su iya yin noma ba kuma lokacin noma zai gaza,” in ji shi a cikin jerin sakonni a kan Twitter.