Siyasa

Rashin Adalci Ne In Ƙi Faɗawa Mutane Buhari Ne Ya Biya Kuɗaɗen Ayyukan Da Ni Ke Yi – Wike

A tsakiyar sa’o’i na yau ne babban lauyan gwamnatin tarayya mai suna Abubakar Malami ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin halartar bikin kaddamar da makarantar koyon aikin lauya da aka gina a karkashin gwamnatin Nyesom Wike.

Dan asalin jihar Ribas na farko ( Nyesom Wike) yace, “mutane da yawa sun yi ta tambaya ta daga ina nake samun kudi don gudanar da ayyuka, to ba adalci ba ne idan ban fada wa jama’a (mutane) kudaden da nake amfani da su ba na ayyuka (Flyovers) da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi kuma ya biya, kudin ne suka ki biyan jihohin Neja Delta tun 1999.”

Gwamna Nyesom Wike ya cigaba da cewa, “Shugaba Muhammadu Buhari ya biya jihohin Ribas, Delta, Akwa Ibom, Edo da Bayelsa kashi 13 cikin 100, shi yasa tun daga shekarar 2019 zuwa yanzu, mun kaddamar da gadar sama ta 9, kuma za mu yi aikin gadar sama. har yanzu na kara kaddamar da gadar sama, ina mika godiyata ga shugaba Buhari ta hannun babban mai shari’a.”

Masu Alaƙa