School Elites Hausa a shirye take ta kare ka bayanan ka a duk lokacin da kake amfani da shafin ta. Domin mu samar maka da dinbin aikace aikacen School Elites Hausa, a wasu lokutan za mu nemi sanin wasu bayanan ka.
Duk lokacin da ka bada wadannan bayanai, muna da ikon yin amfani da su kamar yadda tsarin shari’a na Najeriya ya tanada, wanda ya hada da kundin kare bayanai na tsarin mulkin Najeriya.
Shafin mu yana dauke da rariyar likau dake hada shi da sauran shafuka mallakar wasu. School Elites Hausa ba ta da alhakin abinda ke kunshe a wadannan shafuka wadanda ba mallakar ta ba, don haka idan ka shiga to ka sani kai ka kai kanka ba ruwan School Elites Hausa.
Haka zalika, muna baka shawara a duk lokacin zaka shiga irin wadannan shafukan yana da kyau sosai ka tsaya ka karanta ka’idodin sirrin su (Privacy Policy).
WaÉ—anne Bayanai School Elites Hausa Za Ta Tattara Game Da Ni?
Idan ka amince ka shiga ko ka karbi bayanai daga shafin School Elites Hausa, kamar labarai ta imel, mukala da tattauanawa ko yin tsokaci ta (Comments) ko sakonni, to za mu nemi sanin wasu bayanan ka, kamar suna da imel.
Idan ka rubuta bayanan ka a inda aka nemi ka yi hakan, kamar wajen yin sharhi/ tsokaci ko (Comments) a turance, ka bawa School Elites Hausa da masu yi mata ayyuka damar baka bayanan da ka nema.
Har ila yau School Elites Hausa na amfani da Cookies (Rariyar likau) a harshen hausa. Cookies wata karamar hanya ce ta tattara bayanai game da abinda ka fi so ko sha’awa a shafin mu wanda zai bamu damar juya akalar shafin domin dacewa da abubuwan da kake ra’ayi. Za ka iya sa mashigar Internet dinka ta amince da baki dayan cookies ko kuma su yi watsi da su a kowanne lokaci.
Bugu da kari, muna tattara adireshin IP, (Adireshin IP shi ne lambar da za ta bayyana wata kwamfiyuta a cikin intanet).
Muna amfani da dabarun masu sharhi domin duba adireshin IP da Cookies domin inganta yadda kake amfani da shafin. Wadanann bayanai ba za’a yi amfani da su ba wajen hada bayanan ka na sirri bisa ka’ida.
Za’a kuma dinga share wannan mashigar (cookies) akai akai.
Haka kuma muna amfani da adreshin ka na IP domin sanin ko kana amfani da shafin ne daga ciki ko wajen Najeriya.
Idan shekarun ka ba su haura goma sha uku ba, to ka nemi izinin iyayen ka kafin ka baiwa School Elites Hausa bayanan ka na sirri. Yaran da ba su sami wannan izinin ba to ba su da damar bamu bayanan su na sirri.
Ta Wacce Hanya School Elites Hausa Suke Amfani Da Bayanan Da Suka Samu Dangane Da Ni?
School Elites Hausa za ta yi amfani da bayanan ka ne kawai saboda wasu dalilai, wadanda suka hada “huldar aiki”, abinda ke nufin cewa School Elites Hausa za ta iya tuntubar ka dangane da irin bayanan da ka nema.
Za mu boye bayanan ka cikin sirri, sai inda doka ko shari’a ta nemi a bayyana shi.
Har Tsawon Yaushe Ne School Elites Hausa Za Ta Rike Bayanai Na?
Za mu ajiye bayanan ka a na’urar mu har tsawon lokacin da ya dace domin yin abinda ya dace kuma bisa doka da ka’ida. A lokacin da ka bayar da gudummawa zuwa shafin School Elites Hausa, za mu ajiye bayanan ka har na tsawon lokaci muddin dai akwai bukatar yin hakan.