Siyasa

PDP Ta Maka Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrazaq Kotu Bisa Zargin Shi Da Yin Takardun Bogi

An gurfanar da Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin shi da yin amfani da takardar shaidar kammala karatu ta Yammacin Afirka WAEC, na jabu wajen tabbatar da tsayawa takarar Gwamna a zaben 2023 a Jihar.

A karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kan shi, an bukaci babbar kotun tarayya da ta haramtawa gwamna da jam’iyyar APC shiga zaben gwamna na shekara mai zuwa.

Sabuwar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/22 an shigar da kara ne a madadin PDP ta hannun wani babban Lauyan Najeriya, SAN, Cif Paul Erokoro, kuma har da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Abdulrahman Abdulrasaq da Jam’iyyar All Progressives Congress (APC). ) a matsayin wanda ake tuhuma na 1 zuwa na 3.

An bukaci kotun da ta yi amfani da sashe na 171 da 285 na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 da kuma sashe na 29 na dokar zabe domin soke shigar gwamnan zabe mai zuwa.

PDP ta tabbatar da cewa takardar shaidar kammala karatun sakandare ta WAEC da gwamna ya mika ta hannun jam’iyyar APC don taimaka masa ta kammala karatunsa kamar yadda aka tanada a sashe na 177 na kundin tsarin mulkin 1999 na jabu ne ba nasa ba.

A halin da ake ciki, Mai shari’a Inyang Edem Ekwo ya sanya ranar 28 ga watan Oktoba domin sauraron karar.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi