PDP ta ci amanar Igbo, ƴan Najeriya za su fuskanci sakamakon cin amanar – Ibegbu
A ranar Lahadi ne tsohon mataimakin sakataren yada labarai na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Chuks Ibegbu, ya zargi jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, da cin amanar kabilar Igbo.
Ibegbu ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Da yake magana da jaridar DAILY POST, Ibegbu yace PDP ta yi hannun riga da yanayin kasar inda ta zabi Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Sai dai yace bai kamata yan kabilar Igbo su dogara ga jam’iyyun siyasa ba, sai dai a dogara ga daidaikun mutane idan yankin Kudu maso Gabas ya cimma burin shi na samar da shugaban kasar Najeriya.
A cewar Ibegbu: “Halin da al’ummar kasar ke ciki shi ne mulki ya koma Kudu maso Gabas, kuma sabanin yadda al’ummar kasar ke ciki, PDP ta ci amanar kabilar Igbo, wanda muka biya kudin sabulu don dorewa. PDP ta ci amanar Kudu maso Gabas da Igbo.
“A koyaushe muna ba da shawarar cewa don samar da zaman lafiya, daidaito, kwanciyar hankali, cigaban al’umma, shine mulki ya kamata ya koma yankin Kudu maso Gabas da kuma Igbo baki daya.
“Don haka PDP ta sabawa halin da al’umma ke ciki. Sai dai har yanzu ba a rufe kofar ba; akwai sauran jam’iyyun siyasa. Kuma ina ganin bai kamata mu dogara ga jam’iyyun siyasa ba, a’a ga daidaikun mutane idan muna son ciyar da Nijeriya gaba.
“PDP ta yi nata, kuma ana sa ran sauran jam’iyyu su yi nasu, to yan Nijeriya su yanke shawara idan muna so mu cigaba da zama ginshikin talauci a duniya, yan Nijeriya su yanke shawara idan suna son cigaba da tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin kasar nan.
Rashin tsaro ya fi muni a yankin Arewa maso Gabas, inda Atiku ya fito. Akwai rashin tsaro a Daura, inda Buhari ya fito. Haka nan muna fama da rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas da duk fadin Najeriya.
“Wakilan da suka je babban taron jam’iyyar PDP, suka yanke shawarar karɓar toshiyar baki da kudi, su da ‘ya’yan su za su fuskanci kalubalen gobe idan ba mu daidaita ba.