Labarai

PDP a Ogun ta dage kan Adebutu ne ɗan takarar gwamna

Jam’iyyar People’s Democratic Party PDP a jihar Ogun a ranar Alhamis ta tabbatar da Ladi Adebutu a matsayin dan takarar gwamna a jihar.

Shugaban PDP na jihar, Hon. Sikirulai Ogundele, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abeokuta.

Jam’iyyar ta gudanar da babban taro guda biyu a jere a jihar a ranar 25 ga watan Mayu.

Adebutu ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta yayin da wani dan takarar gwamna, Mista Segun Sowunmi, ya zama dan takarar jam’iyyar PDP a babban taro na biyu da aka gudanar a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Abeokuta a ranar.

Dan takara na uku, Mista Jimi Lawal, a kwanakin baya ya bukaci shugabannin jam’iyyar na kasa da su soke zaben fidda gwani na gwamna da Adebutu ya lashe tare da shirya wani atisayen zabar wanda zai rike mata tuta a jihar.

A wajen taron, Ogundele ya bayyana cewa zaben fidda gwani da ya samar da Adebutu da sauran ‘yan takara an gudanar da shi ne bisa ka’idojin zabe da ka’idojin jam’iyya.

Yace: “Zaben fidda gwani na gwamna da aka gudanar a Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) kamar yadda ofishin na kasa ya amince da shi a ranar 25 ga watan Mayu, ya fitar da dan takara daya tilo a jam’iyyar mu, kuma shi ne Hon. Oladipupo Adebutu wanda ya samu kuri’u 714.

Masu Alaƙa