Labarai

Orubebe ya koma APC shekara bakwai bayan ya nuna adawa da nasarar Buhari a zaben 2015

Tsohon ministan harkokin Neja Delta Godsday Orubebe ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

Tsohon ministan ya fice daga jam’iyyar PDP ne a ranar 20 ga watan Yuni.

Ya koma jam’iyyar APC ne sama da shekaru bakwai bayan yayi yunkurin hana shugaba Muhammadu Buhari yin tattaki zuwa nasara a zaben shugaban kasa na 2015.

Orubebe ya haifar da ce-ce-ku-ce a lokacin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.

Tsohon Ministan ya tashi daga kujerar da yake zaune a cibiyar tattara sakamakon zabe, ya zagaya zuwa zauren taro, ya kwace makirufo sannan ya zauna a kasa yana nuna rashin amincewa da sakamakon da aka bayyana wanda ya bai wa ‘yan kallo mamaki ciki har da tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa. Hukumar (INEC), Farfesa Attahiru Jega.

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Burutu ta jihar Delta, Moni Seikemienghan Moni, wanda ya tarbi Orubebe zuwa jam’iyyar a ranar Juma’a, ya bayyana tsohon ministan a matsayin babban abin ci gaba a jam’iyyar.

Masu Alaƙa