Al'umma

Nnamdi Kanu: A Shirye Muke Mu Gamu Da Gwamnatin Tarayya A Kotun Koli – IPOB

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta bi hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ranar 13 ga Oktoba, 2022 na sakin Nnamdi Kanu.

Sai dai kungiyar ta ce a shirye take ta gamu da gwamnatin Najeriya a kotun koli a ranar Litinin 24 ga watan Oktoba, 2022.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na IPOB, Emma Powerful ya fitar, IPOB ta nanata cewa babu wata barazana ko tsoratarwa da za ta sa ta ja da baya daga aikin dawo da kasar Biafra.

Ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da sauran kasashe masu wayewa da su gargadi Gwamnatin Najeriya da Jami’an tsaron ta da su bar kasar Biafra ita kadai.

Kungiyar ‘yan awaren ta kuma zargi jami’an tsaro da alhakin toshe hanyoyin da manyan motoci suka yi domin a sako shugaban su, Mazi Nnamdi Kanu.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi

Duba Kuma
Close