Labarai

Nasarorin Da Sean Dyche Ya Samu Daga Ɗan Wasa Zuwa Koci

A matsayin shi na dan wasa, Sean Dyche ya kasance mai tsaron baya na tsakiya kuma ya sami daukaka tare da kungiyoyi uku (Bristol City, Millwall da Northampton Town). A matsayin shi na manaja, ya sami cigaba tare da Burnley a lokuta daban-daban guda biyu.

Bayan ya taba zama kocin Watford, an nada shi kocin Burnley a shekarar 2012. A halin yanzu shi ne koci mafi dadewa a gasar Premier. Kuma tare da Jurgen Klopp da Pep Guardiola, yana daya daga cikin kocin Premier uku a halin yanzu da suka shafe sama da shekaru biyar a kungiya daya.

An nada Dyche a matsayin kocin Premier na watan a Maris 2018 da Fabrairu 2020.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi