Siyasa

Mutane Da Dama Sun Samu Raunuka, Bayan Ƴan Daba Sun Kai Wa Ayarin Motocin Kamfen Ɗin Atiku Hari

Rahotanni sun ce an kwantar da mutane da dama a asibiti yayin da wasu ‘yan daba da ba a san ko su waye ba suka kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a Maiduguri babban birnin jihar Borno a ranar Laraba.

Dino Melaye, kakakin jam’iyyar PDP ne ya bayyana haka a wani gangamin yakin neman zabe a jihar.

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa, an lalata motoci kasa da 100 a harin.

Ya zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da yunkurin kawo cikas ga yakin neman zaben jam’iyyar adawa.

Yace: “Sun tura ‘yan barandan su ne suka kai wa ayarin motocin mu hari da duwatsu, sanduna, adduna yayin da muka fito daga fadar Shehu domin zuwa dandalin Ramat, duk a kokarin su na hana taron mu.

“An baza ‘yan daba a wurare da dama don kai wa magoya bayan mu hari. Amma muna so mu tabbatar musu cewa babu wanda zai iya hana mu”.

Masu Alaƙa