Labarai

Mawakin Annabi [S.A.W] Ya Kashe Iyayen Shi Akan Zargin Ɓatanci Ga Annabi

Munkaila Ahmadu wanda ya kashe iyayen shi a karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa yace yayi hakan ne saboda sun yi kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

Malam Ahmadu, mawaki kuma dan darikar Tijjaniyya, yace iyayen shi sun yi masa ba’a da cewa shi mahaukaci ne kuma suna adawa da kasancewar shi mawakin yabo ga Annabi Muhammadu (S.A.W).

Arewa Post ta ruwaito yadda ƴan sanda a jihar suka kama Mista Ahmadu, mai shekaru 37, bayan ya kashe iyayen shi tare da raunata wasu mutane biyu ranar Alhamis.

Yayi amfani da kwarkwasa wajen kashe mahaifin shi, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, wanda shine hakimin kauyen Zarada da ke yankin karamar hukumar Gagarawa, da mahaifiyar shi Ahmad Hauwa’u, mai shekara 60.

A wani faifan bidiyo da aka nada a hannun ƴan sanda da PREMIUM TIMES ta samu, Mista Ahmadu yace bai yi nadamar abin da ya aikata ba domin an umarce shi da yayi hakan.

“Na kashe su ne saboda sun ki yarda da gaskiya game da Annabi Muhammad (S.A.W). Na kashe su ne saboda zagin Annabi kuma hukuncin su kisa ne, babu tuba ga duk wanda ya zagi Annabi.

“Ni mawakin yabo ne ga Annabi, bana niyyar yin bidiyo don wakata kuma in sha Allahu zan yi haka, zan samu ƴanci domin Allah yana tare da adali, shi yasa ban damu da komai ba,” in ji Mista Ahmadu a wani faifan bidiyo da ƴan sandan suka dauka.

“Iyayena ba sa son Annabi Muhammad (S.A.W) saboda ina kaunar shi, sun ce min mahaukaci ne, na roki mahaifina ya tallafa min (Wakar yabo), kuma na ce masa ba na so. Ni ba ɗan caca ba ne, ba na shan ƙwayoyi, kuma ba na yin sata, amma ya ƙi.

“Mahaifiyata ta kasance tana zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ni don ta bata min rai, tana gaya wa mutane su ki ni duk lokacin da na zo wakar yabon Annabi saboda na haukace kuma na ki yin aikin gona.

“Yanzu ina hannun ƴan sanda saboda a tunanin dan Adam na yi abin da bai dace ba amma a wurin Allah da Annabi abin da na yi shine daidai,” in ji Mista Ahmadu.

Mista Ahmadu, wanda yake da ƴaƴa biyar, yace kuma yana zargin mahaifin shi da yin lalata da matar shi.

Masu Alaƙa