Siyasa

Matar Osinbajo Na Cikin Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima – Inji APC

Jam’iyyar All Progressives Congress APC, ta ce ba a cire matar mataimakin shugaban kasa, Misis Dolapo Osinbajo daga cikin tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar ba.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne jam’iyyar da ke mulkin kasar ta sanar da jerin sunayen jirgin yakin neman zaben mata karkashin jagorancin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari; uwargidan dan takarar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu; da matar dan takarar mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima.

Jerin yakin neman zaben wanda ya kunshi sunayen manyan mata 944 da aka yiwa lakabi da ‘Tinubu-Shettima Women Presidential Campaign Team’, A’isha Buhari a matsayin babban a kungiyar, da Tinubu, Sanata mai wa’adi uku, a matsayin shugaba, amma sunan matar Osinbajo Dolapo ya ɓace.

Idan dai za a iya tunawa, ba a saka mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a cikin kwamitin yakin neman zaben Tinubu da Shettima ba, matakin da shugabancin majalisar ya rataya ne a kan umarnin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya bar Osinbajo da Mustapha su mayar da hankali kan mulki.

Sai dai da take zantawa da manema labarai, shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa, Dokta Betta Edu, ta ce uwargidan mataimakin shugaban kasar na taka rawar gani a yakin neman zaben shugaban kasar.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi