Makiyaya Sun Kai Hari: An Gano Gawarwaki 36, Mutane Da Dama Sun Bata A Benue

Akalla gawarwakin mutane 36 ne aka gano yayin da wasu da dama kuma ba a gan su ba bayan harin da wasu da ake zargin Fulani ne da ke dauke da makamai suka kai a safiyar ranar Laraba, a kauyen Gbeji da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.
An bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da gwamnan jihar, Samuel Ortom, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Anthony Ijohor, Sanata mai wakiltar mazabar Benuwe ta Arewa maso Gabas, Gabriel Suswam, kakakin majalisar dokokin jihar Benue da kuma dan takarar gwamnan PDP, Engr Titus Uba da sauran su sun ziyarci al’ummar.
Da yake jawabi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da sauran wadanda suka tsira yayin ziyarar, Gwamna Ortom wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Anthony Ijohor, SAN, ya bayyana bakin cikin shi kan wannan mummunan lamari.
Ya kara jaddada matsayar gwamnatin jihar Binuwai cewa tunda gwamnatin tarayya ta gaza wajen samar da tsaro ga jama’a, ya kamata a baiwa gwamnatin jihar lasisin siyo nagartattun makamai ga yan banga na al’umma domin kare jama’a.
A cewar Ortom, iyakokin hukumomin tsaro na al’ada sun yi yawa kuma sun kasa ba da cikakkiyar kariya ga mutanen jihar.
“Muna nan kan bukatar mu na neman Gwamnatin Tarayya ta ba mu lasisin ƴan bangar mu na sa kai su rike AK-47 da sauran manyan makamai. Jami’an tsaro sun yi yawa, don haka lamarin ya zama dole mutanen mu su kare kan su,” inji shi.
Gwamna Ortom ya bukaci matasa da su tsaya tsayin daka wajen kare filayen su, inda ya bayyana cewa taimakon kai ne kawai abin da ya rage, tunda gwamnati mai ci a cibiyar ta nuna cewa ba ta iya samar da tsaro ga jama’a.
Ya jajanta wa wadanda suka rasa ‘yan uwan su a harin da aka kai wa Gbeji, ya kuma kara musu kwarin guiwa da kada su karaya ko da halin da ake ciki, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta samar da agajin jin kai don tallafawa wadanda abin ya shafa.
Sanata Suswam a nasa jawabin, ya caccaki gwamnatin tarayya kan abin da ya bayyana a matsayin rashin dawainiya da gazawarta wajen samar da tsaro ga ‘yan kasa.
A cewarsa, “Gwamnatin Tarayya ta gaza sosai wajen kare rayuka da dukiyoyi”, inda ya koka da yadda rashin tsaro ya fallasa tsiraicin kasar.
“Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 36 daga wannan mummunan harin da makiyaya suka kai. Wannan ba shi da karbuwa kwata-kwata ta kowane ma’auni. Hakan ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da ta sha alwashin kare su.
“Abin da wannan ke nufi shi ne, an mika mulki ga wadanda ba na gwamnati ba. Su ne kwata-kwata a yanzu kuma suna zuwa su kashe mutane yadda suke so su tafi cikin walwala kuma ba a taba kama wani mutum ba,” in ji shi.