Maganin Kurajen Fuska Na Gargajiya [Pimples]

Ba ku tunanin mafi munin mafarkin kowace yarinya shine pimples?
Ba wai kawai suna lalatar da fuskarka ba, har ma suna haukatar da kai tare da rashin jin daɗi na yau da kullum.
Abu mafi ban haushi game da pimples shine suna yawan bayyana lokacin da kuke tsammanin su kaɗan.
Idan kun gwada samfuroran magunguna da yawa na kasuwa kuma kun kasa kawar da su, wannan shine wurin da zai iya fitar da ku daga matsala. Anan akwai magungunan gargajiya na pimples.
Domin kawar da kurajen fuska sa makamantan su da suka addade ku, kuna bukatar haɗa wandannan abubuwan da zamu lissafa a ƙasa:
- Garin habbatus-sauda (Black seed)
- Man zaitun (Olive oil)
- Ruwan Khal (Ma’u Khal)
Idan an samu waɗancan abubuwan na sama, za’a ƙwaɓa garin na Habbatus-sauda da ruwan Khal dai-dai gwargwado, kuma kada haɗin yayi ruwa sosai.
Bayan an garwaya Habbatus-sauda da ruwan Khal ɗin, sai a ɗauko man zaitun ɗin da muka ambata a zuba gwargwado a cikin haɗin a sake garwaye sosai har yayi ruwa-ruwa ta yadda za’a iya shafa shi.
Za’a zuba wannan haɗin a cikin wani kwalba ko gwango sai a kai shi ga rana ya samu kamar awa ɗaya.
Yadda za’a yi amfani da shi:
Za’a riƙa shafa wannan haɗin a wuraren da kurajen suka fito da dare idan za’a kwanta da kuma da safe in an tashi daga barci.
Domin samun sauki cikin kankanin lokaci, ya kamata a riƙa wanke wurin da abin shafa sosai kafin shafa wannan haɗin.
Karin fa’idodin haɗin:
Wannan haɗin ba wai kawai yana kawar da kurajen fuska kaɗai ba, yana warkar duk wata matsalar fata kama daga maƙero kyasbi da sauran matsalolin fata da yardar Allah.