Al'umma

Mafarauci Ya Kashe Kan Shi Saboda Ya Samu Saɓani Da Mahaifiyar Shi

Wani mafarauci a jihar Adamawa, Usman Audu, ya harbe kan shi har lahira bayan wata ‘yar rashin jituwa tsakanin shi da mahaifiyar shi.

Majiyoyin yankin da suka bayyana lamarin a ranar Asabar din da ta gabata sun ce, Usman dan ’yan banga ne a yankin, ya sha da kyar ne daga hannun mahaifiyar shi bayan ya lakada wa dan nasa duka saboda ya dawo daga wani aiki da yayi a makare.

Audu wanda dan asalin Gada Maisaje ne a karamar hukumar Gombi, ya yiwa yaron shi dan shekara hudu bulala da sanda bisa zargin shi da yin wasa da wasu yara tare da jinkirta dawowar shi gida daga wata sana’a.

Mahaifiyar shi kuwa tana kallon hukuncin da aka yiwa jikanta a matsayin mai tsauri, ta gaya wa Audu haka.

Wata majiya ta ce da alama Audu ya ga tsantsan da mahaifiyar shi ta yi masa ba abin yarda ba ne, kuma ya mayar da martanin da bata zata ba, inda ya shaida wa mahaifiyar shi cewa zai kashe kan shi ya bar mata duniya.

“Sai ya je ya nemi bindigar shi ta banga ya harbe kan shi a ciki,” in ji daya daga cikin majiyoyin.

An ce an garzaya da Audu asibiti inda likita ya tabbatar da rasuwar shi.

Majiyar, wacce ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, ta kara da cewa: “Al’umma har yanzu suna mamakin matakin Usman (Audu).

“Har yanzu mutane suna mamakin dalilin da yasa zai kashe kan shi saboda mahaifiyar shi ta gargade shi da kada ya doke dan shi.”

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi