Kotun Kolin Najeriya Ta Amince Da Sanya Hijabi A Makarantun Jihar Legas

Kotun kolin Najeriya a ranar Juma’a a Abuja ta amince da amfani da hijabi ga dalibai mata musulmi a makarantun gwamnatin jihar Legas.
Gwamnatin jihar Legas dai ta haramta sanya hijabi, inda ta ce ba ya cikin tufafin makarantar da aka amince wa dalibai mata su yi amfani da su.
Bayan dakatarwar, daliban Musulmai sun shigar da kara a ranar 27 ga Mayu, 2015, suna neman kotu ta ayyana haramcin a matsayin cin zarafin su na yancin tunani, addini da ilimi.
Shari’ar, msi lsmva CA/L/135/15, ta kasance tsakanin gwamnatin jihar Legas, Miss Asiyat AbdulKareem (ta hannun mahaifin ta), Miss Moriam Oyeniyi da kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya.
A hukuncin da kotun ta yanke, ta yi watsi da daukaka karar da gwamnatin jihar Legas ta shigar, sannan ta amince da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a baya wanda ya haramta hijabi na nuna wariya ga dalibai musulmi a jihar.
Alkalan da ke cikin kwamitin sun hada da Justice Olukayode Ariwoola, Justice Kudirat Kekere-Ekun, Justice John Inyang Okoro, Justice Uwani Aji, Justice Mohammed Garba, Justice Tijjani Abubakar, da Justice Emmanuel Agim.
Kwamitin alkalan ya cigaba da cewa, abin da daliban musulmi suka bayyana a kan haramcin ya keta hakkin su na yancin tunani, lamiri, addini, mutuncin dan Adam da yancin da kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya ba su.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Amir na MSSN a jihar Legas, Miftahudeen Thanni, ya bayyana farin cikin shi da wannan cigaba, inda ya kara da cewa hakan zai baiwa daliban makarantun firamare da sakandire na gwamnati a jihar Legas su sanya hijabi zuwa makaranta ba tare da tsangwama ba.