Laifuka

Kotu Ta Tasa Keyar Dan Takarar Sanata Na Labour Party, Okorie Zuwa Gidan Yari

Wata babbar kotu da ke zamanta a Abakaliki a ranar Talata ta tasa keyar dan takarar Sanatan Ebonyi ta Kudu na jam’iyyar Labour Party, LP, Linus Okorie, a gidan gyaran hali.

An gurfanar da Okorie a gaban kotu kan tuhume-tuhume biyar da suka hada da labaran karya, kisan kai, hulda da masu safarar miyagun kwayoyi da kuma wasu tuhume-tuhume guda biyu.

Dan sanda mai shigar da kara, Chinagorom Ndubuaku, wanda ya gabatar da tuhume-tuhumen da ake yiwa tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, yace wanda ake tuhuma yana cikin jerin sunayen ‘yan sanda da ake nema ruwa a jallo saboda aikata laifuka daban-daban.

A martanin da ya mayar, babban lauyan wanda ake kara, Mista Chika Nomeh, wanda ya zanta da manema labarai jim kadan bayan kotun yace; “Wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake zargin sun yiwa alkali damar yin la’akari da bayar da belinsa, sakamakon haka, alkalin kotun ya cigaba da tsare shi (Okorie) a cibiyar gyara Najeriya.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi