Kisan Aisami: Abinda Buhari Ya Nemi Rundunar Soji Ta Yiwa Sojojin Da Suka Kashe Limamin Yobe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da kisan da aka yiwa wani Malamin addinin Islama wanda a halin yanzu ke samun martani daga ƴan Najeriya.
A nasa jawabin, Buhari yayi kakkausar suka kan kisan da aka yiwa malamin addinin Islama na jihar Yobe wanda aka fi sani da Sheikh Goni Aisami. A cewar wani rahoto da Daily Post ta wallafa, daga nan ne shugaba Buhari ya umarci sojojin Najeriya da su gaggauta hukunta wadanda suka aikata wannan aika aika. A matsayin hanyar daukar matakan da suka dace, ya kuma umurci hukumomin soji da su kawar da wasu baragurbi daga cikin su da ke da irin wannan dabi’a.
A cewar rahoton da aka ambata a sama, an ce daya daga cikin sojojin da ya bayar da tayin ne ya kashe malamin kamar yadda ƴan sanda suka tabbatar. Buhari wanda ya yi magana ta bakin daya daga cikin mai magana da yawunsa, Gaba Shehu, ya bayyana cewa irin wannan mugun aiki ba shi da wani matsayi a soja ko kadan. Ya kara da cewa an horar da mazan sojojin Najeriya da su zama masu ladabtarwa, da kare rayuka, da mutunta tsarkin rayuka da kuma kada su jefa rayuka cikin hadari.
Ya kara da cewa a matsayin shi na babban kwamandan sojojin Najeriya, yayi Allah wadai da kisan saboda rashin tausayi yana mai cewa irin wannan abu na iya sa fararen hula su ji tsoron sojoji kuma hakan na iya sanya su zama masu gaba da mazan rundunar. Shugaban ya mika ta’aziyyar shi ga iyalan marigayin, gwamnati da kuma al’ummar jihar Yobe bisa rasuwar malamin.
Menene ra’ayinku akan wannan labarin?