Labarai

Jihar Kwara Amince Da Sanya Hijabi Sayan Sake Buɗe Makarantar Baptist

Bayan rufewa na tsawon watanni hudu saboda dalibai mata musulmi masu sanya hijabi, gwamnatin jihar Kwara ta sanar da bude makarantar sakandare ta Oyun Baptist dake Ijagbo ga dalibai.

A ranar Alhamis, 3 ga Fabrairu, 2022, gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantar, inda ta bayyana cewa ta “yi Allah-wadai da matakin nuna wariya ga kowa, musamman kananan yara, kan dalilan addini.”

“Ba za’a amince da irin wannan wariyar ba a kowane mataki ba,” in ji gwamnatin Kwara.

Misis Mary Adeosun, babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi da cigaban bil’adama ta jihar, ta sanar da cewa makarantar za ta dawo ranar Juma’a 3 ga watan Yuni, daidai da watanni hudu da rufe makarantar, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.

Gwamnati ta ce ba za ta “yi jinkirin sake rufe makarantar ba, da dai sauran su, idan wani abu ya kawo barazana ga lafiyar kananan yaran”.

Sanarwar ta ce, “Shawarar da ma’aikatar ta yi na sake bude makarantar na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati ta bi don dawo da zamanta a makarantar.

“Saboda haka, an umurci dukkan malamai da dalibai da su koma azuzuwan su yayin da kwamitin farar takarda na gwamnati ke cigaba da kokarin magance matsalolin da ke kan gaba da suka shafi hargitsi a makarantar gwamnati.

“Hakazalika, ma’aikatar ta sake jaddada matsayin gwamnati na cewa duk wata ‘yar makaranta musulma da ke da sha’awar sanya hijabi, an ba ta damar yin hakan a dukkan makarantun gwamnati, ciki har da makarantar sakandare ta Oyun Baptist ta Ijagbo, wadda mallakin gwamnatin jihar ne da dukiyar al’umma. ”

Masu Alaƙa