ISWAP Ta Kashe Ƴan Boko Haram 8, Ta Ƙwace Makamai Masu Yawa

Kimanin ‘yan ta’adda takwas ne rahotanni suka ce an kashe a lokacin da mayakan Boko Haram suka yi arangama da ‘yan kungiyar IS da ke yankin yammacin Afirka (ISWAP) na ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi.
Rundunar ta ISWAP ta kuma kama manyan harsasai a rikicin ‘yan hamayyar da ya faru a ranar 6 ga watan Oktoba, lokacin da wata tawagar kungiyar ta ISWAP ta kai hari tare da yiwa abokan gabarta mummunar barna a yankin Krinowa da ke Arewa maso Gabashin Marte a jihar Borno.
Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi cewa mayakan Boko Haram 12 na dawowa daga Marte bayan karbar makamai masu yawa daga sansanin Amir Jay na Boko Haram, Bakura Wulgo.
Kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnah Lid-Da’awah wa’l-Jihad ta Boko Haram ta aike da tawagar mutane 12 daga Gaizuwa a garin Bama domin neman makamai bayan sun sha mumunar kashi da asara sakamakon ci gaba da suka yi. Hare-haren na sama da hukumar leken asiri ke jagoranta, da harin bama-bamai da manyan bindigogi da kasa, hare-haren da sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai ke kaiwa.
‘Yan ta’addan Boko Haram da suka mamaye Gaizuwa, wanda aka fi sani da Gabchari, Mantari da Mallum Masari, sun yi asarar kusan dukkanin makamansu, motoci da babura, lamarin da ya sa mayakan da suka lalace suka shiga cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren da sojojin Najeriya ke kaiwa, da kuma mayakan ISWAP da ke karkashin jagorancin Ba’.