Labarai

Hotuna: Ƴan Sanda Sun Kama ASP Mai Shekaru 43 Na Bogi A Akwa Ibom

Wani matashi mai suna Vincent Sampson Enuneku daga karamar hukumar Ndokwa ta jihar Delta ya shiga hannun jami’an rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom bisa zargin shi da shigar burtu da kuma zargin mallakar tabar wiwi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan Mista Odiko MacDon, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne a garin Uyo a lokacin da yake kokarin yin amfani da katin shaidar sa na bogi na mataimakin Sufeton ƴan sanda (ASP) domin dakile kama wanda ake nema ruwa a jallo.

A cewar MacDon, wanda ake zargin yayi amfani da katin shaidar karya ne don wucewa ta wuraren bincike cikin sauki yayin da yake shigowa da wiwi ta Indiya da sauran kayayyakin da aka haramta.

Ya kara da cewa, Mista Olatoye Durosinmi, kwamishinan ƴan sandan jihar, ya kara wa mataimakan sufiritandan ƴan sanda 37 karin girma zuwa mukamin sufiritandan ƴan sanda (SP), amma kuma ya bayar da gargadi ga duk wanda ke yin kwaikwayon ƴan sanda da sauran kungiyoyin tsaro da su daina nan take.

Masu Alaƙa