Labarai

Harbe-harbe: Rikici ya ɓarke tsakanin Fulani da ƴan ƙungiyar OPC

Rikici ya barke a ranar Juma’a tsakanin Fulani da ƴan kungiyar Oodua Peoples Congress (OPC) a Ajase Ipo, karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara.

An yi ta harbe-harbe a yayin da aka kai wa motocin da ke bi ta babbar hanyar hari.

An tattaro cewa fadan ya fara ne a kasuwar Kaara, Ajaase Ipo a yammacin ranar Juma’a.

Jami’in hulda da jama’a na ƴan sanda a jihar Kwara, Ajayi Okasanmi ya shaidawa DAILY POST ta wayar tarho cewa an tura jami’an tsaro zuwa wurin.

A cewar shi, ba za a iya tantance adadin wadanda suka mutu ba kamar yadda a halin yanzu.

Masu Alaƙa