Labarai

Hanyoyi 6 Domin Kiyaye Kamuwa Da Cutar Basir Ko Ɗan Kanoma

Basir ko ɗan kanoma wanda ake kira da “hemorrhoids” ko kuma “piles” a harshen turance, cuta ce da ke cigaba da yiwa gurguwar fahimta a tsakanin al’umma.

A likitance, ba wani abu ne basir ba ko ɗan kanoma face kumburarrun jijiyoyin jini ƙarshen babban hanji (Large Intestine) da kuma dubura (Anus). Waɗannan kumburarrun jijiyoyin jini su ne suke talewa har su yi bulli cikin ƙarshen babban hanji ko kewayen dubura.

Ɗan kanoma ƙarshen babban hanji shi ne “basir na cikin dubura” yayin da basir a kewayen dubura shi ne “basir na wajen dubura”. Haka nan, “basir mai tsiro” habakar “basir cikin dubura” ne wanda ke bayyana yayin da matsalar ta je matak na ƙarshe.

“Basir mai tsiro” na wakana ne bisa dalilin zazzagowa ko saukowar jijiyoyin jinin da suka kumbura zuwa wajen dubura, musamman yayin yunƙurin bayan gida ko wani mai kama da wannan.

Alamomin Bayyanar Basir/Ɗan Kanoma

Bayyanar alamomin basir ya danganta ne ga wane irin basir ne ya ɓulla, “basir cikin dubura” ko kuma “basir a wajen dubura”.

Alamomin “Basir A Cikin Dubura”

1. Zubar jini ba tare da jin ciwo ba yayin tsuguno ba.

2. “Basir mai tsiro” wanda ke fitowa wajen dubura har sai an tura da yatsa domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da raɗaɗi.

Alamomin “Basir A Wajen Dubura”

1. Ciwo mai raɗaɗi

2. Ƙaiƙayi

3. Kumburi a kewayen dubura

4. Zubar jini yayin yunƙurin tsuguno/bayan gida ko bahaya.

Sabubban Da Ke Kawo Basir/Ɗan Kanoma

Basir na faruwa sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura har su kumbura/haushi sannan su yi ƙololo saboda abubuwa kamar haka:

1. Yawan yunƙuri yayin tsuguno.

2. Tsawaitar lokacin tsuguno.

3. Fama da atini ko kuma taurin bayan gida tsawon lokaci

4. Kasancewa mai Ƙiɓa / teɓa

5. Kasancewa mai juna biyu

6. Cin abincin mai ƙarancin dusa, harza ko ganyayyaki

7. Ɗaga nauyi akai-akai da sauransu

Hanyoyin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi

Hanya mafi inganci wajen kiyaye kai daga kamuwa da cutar basir ko ɗan kanaoma ita ce sanya bayan gida ya zamo mai taushi yadda zai fice ba tare da wani babban yunƙuri ba.

Waɗannan hanyoyi za su taimaka wajen kiyaye kai daga basir da kuma rage matsalolinsa:

1. Cin Abinci Mai Dusa Sosai:

Abinci mai dusa sun haɗa da ƴaƴan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi.

2. Shan Isashshen Abin Sha:

Shan isashshen ruwa aƙalla lita 2 zuwa 3 kowace rana da sauran ababen sha masu ruwa-ruwa.

3. Rage Yunƙuri Yayin Ysuguno/Bahaya:

Yunƙuri tare da riƙe numfashi yayin tsuguno na takura jijiyoyin jini a cikin dubura.

4. Hanzarta Shiga Ban Ɗaki Da ZararNAn Ji Bayan Gida:

Yin buris da bayan gida yayin da aka ji shi na janyo jiki ya ci gaba da tsotse ruwan bayan gidan har ya yi tauri.

5. Atisaye/Motsa Jiki Akai-Akai:

Atisaye ko motsa jiki na taimakawa rage taurin bayan gida. Haka nan, atisaye na taimakawa wajen rage ƙiba wanda hakan zai rage nauyi ko takura ga jijiyoyin jini a cikin dubura.

6. Ƙaurawa Dogon Zama Yayin Bayan Gida:

Dogon zama musamman yayin tsuguno na ƙara takura jijiyoyin jini a dubura.Basir larura ce da ake warkewa sumul bayan amfani da magunguna da sauran hanyoyi a likitance.

Amma idan basir yayi tsanani yin tiyata na iya zama tilas. Tuntuɓi likita da zarar alamun basir sun bayyana maimakon shan magungunan gargajiya da ba ka da tabbacin ingancin su.

Masu Alaƙa