Labarai

Gwamnonin Najeriya Sun Bayar Da Kyautar Miliyan ₦50 Ga Waɗanda Harin Coci A Ondo Ya Shafa

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayar da gudummawar Naira miliyan ₦50 ga wadanda harin ya rutsa da su a cocin St. Francis Catholic da ke titin Owa-luwa a karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Shugaban kungiyar NGF kuma gwamnan jihar Ekiti, Dr. John Kayode Fayemi ne ya bayar da wannan gudummawar a lokacin da ya kai wa Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ziyara a gidan gwamnati ranar Litinin da ta gabata a Akure.

Fayemi ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Ogun kuma Sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya, Sanata Ibikunle Amosun.

Daga baya Akeredolu ya jagorance su zuwa gidan Bishop na cocin Katolika na Ondo, Bishop Jude Arogundade, kafin su wuce Owo domin yi wa Olowo na Owo, Oba Gbadegesin Ogunoye ta’aziyya a fadar shi.

Fayemi, wanda ya bayyana harin a matsayin wanda ba a za’a lamunta ba, ya bayyana cewa Owo ta kasance wuri mai zaman lafiya.

“Hare-hare ne masu tsanani da ba a saba gani ba a kan mutanen da ba za su iya fita gona ko bautar Allah cikin kwanciyar hankali ba. Dukkan mu mun gigice.

“Kamar yadda gwamnan yace, za a hukunta wadannan mutanen. Za a farauto su, a kai su ga kuliya. Amma hakan ba zai iya ceton rayukan da aka yi hasarar ba ko kuma ceto wadanda suka jikkata daga rashin jin dadi.

“A matsayin mu na shugabannin jama’a, za mu rubanya kokarin mu. Wannan yana faruwa a fadin lardin kuma mun damu. Mun san yadda za ku damu. Kuma mun san cewa wannan abu ne da ke damun zukatan mu.

“A yanzu haka, gwamnatoci a matakin jiha da tarayya na kokarin ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin.

“Takwarorina na kungiyar Gwamnonin sun nemi in bayar da gudummawar Naira miliyan ₦50 ga cocin Katolika don inganta yanayin iyalan wadanda abin ya shafa. Wannan laifi ne ga bil’adama.” Fayemi yace.

Bishop na Ondo Diocese, Bishop Jude Arogundade ya bayyana harin a matsayin mugun abu.

Ya bukaci gwamnonin da su tabbatar an gurfanar da wadanda ke da hannu a kisan da masu daukar nauyin su.

Masu Alaƙa