Ƙetare

Gwamnatin Najeriya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Sauya Dokokin Ƙasar Habasha Akan Biza

A jiya Alhamis gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin Habasha (Ethiopia) ta sauya manufofinta na biza.

A ranar Talata ne kasar Habasha ta sanar da dakatar da biza ta kan manufofin shigowa kasar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar game da lamarin, kamfanin jirgin na Habasha yace ana sa ran matafiya daga Najeriya za su samu bizar su a ofishin jakadancin Habasha da ke Abuja kafin yin tafiya zuwa kasar.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Francisca Omayuli ta fitar, gwamnatin tarayya ta ce gwamnatin Habasha ta dauki matakin ne domin inganta tsaro a kan iyakokin kasar.

Gwamnatin ta kara da cewa matakin ba wai ya shafi ‘yan Najeriya ne kawai ba, har sa dukkan baki da ba ‘yan kasar ba da ke shiga kasar ta Habasha.

Gwamnatin tarayya ta bayyana fatan ganin an sake duba wannan manufa idan al’amuran tsaro suka inganta a yankin Arewacin kasar nan.

Sanarwar ta cigaba da cewa: “Dakatarwae ta shafi dukkan ‘yan kasashen da ke dauke da fasfot, wadanda ke neman shiga kasar Habasha ba kawai ‘yan Najeriya ba.

“Hukumomin Habasha sun yi bayanin cewa matakin na da nufin inganta iyakoki na zirga-zirgar mutane zuwa Habasha saboda rikicin da ke faruwa a Arewacin kasar.

“An gayyaci jama’a da su lura da sabon tsarin biza na Gwamnatin Tarayya ta Habasha kuma a yi musu jagora yadda ya kamata.”

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi