Siyasa

Gwamnan Zamfara Ne Ya Kitsa Cire Ni Daga Lambar Yabo Ta Ƙasa – Inji Ɗan Takarar PDP

Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP a 2023 Dr. Dauda Lawal Dare ya zargin gwamna Bello Mohammed Matawalle da kitsa yunkurin cire shi daga jerin lambar yabo ta kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai a Gusau Lahadi.

A cewar shi, kwamitin bayar da lambar yabo ta kasa da shugaba Buhari ya kafa ya zabo shi ne bisa cancanta amma ranar da za a yi bikin, sai kawai ya ji an rasa sunan shi a jerin sunayen.

A cewar shi, ya zartas da duk wani binciken kwamitin tsaro da hukumar bayar da lambar yabo ta kasa kan lamarin.

Ya kara da cewa “An ba ni wasikar sanarwa daga kwamitin kuma na amsa gayyata cikin gaggawa amma abin takaici, kwana daya kafin bikin sai na ji sunana ya bace daga cikin wadanda aka zaba na kasa,” in ji shi.

Ya kalubalanci gwamna Bello Mohammed Matawalle kan kokarin shi na ganin ba a sanya sunan shi a cikin wadanda suka ci kyautar kasa ba.

“An sanar da ni cewa Gwamna Matawalle ya gana da kwamitin da kan shi ya roki a cire ni a kan abin da yace, ni makiyin shi ne kuma na APC.” Inji Dauda.

Dangane da manufar shi da hangen nesa Dr. Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa idan aka ba shi wannan aiki, zai mayar da hankali ne kan tsaro, ilimi, samar da lafiya, aikin yi, karfafa dan Adam amma kadan.

“Bisa la’akari da halin da ake ciki a duk sassan tattalin arzikin da na ambata a baya a jihar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle, zan tabbatar da cewa an farfado da martabar jihar da ta rasa a dukkanin sassan tattalin arzikin kasar idan na zama Gwamnan jihar ya zo 2023 karkashin PDP,” in ji Dokta Dauda.

Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP da magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da su kasance masu bin doka da oda tare da nisantar duk wata annoba da ka iya haifar da tarzoma a lokacin yakin neman zabe, zabe da sauran su.

Masu Alaƙa

Rubuta Sharhi