Labarai

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya janye wa Tinubu

Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Progressives Forum, John Feyemi, ya fice daga takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC.

Fayemi ya nemi magoya bayan shi da su zabi Bola Ahmed Tinubu, babban jigon jam’iyyar na ƙasa.

Fayemi ya bayyana ficewar shi ne a yayin babban taron jam’iyyar na kasa da na yan takarar shugaban kasa a Abuja ranar Talata.

Fayemi, wanda yana daya daga cikin yan takarar shugaban kasa biyar da gwamnonin jam’iyya mai mulki suka mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce sun yanke shawarar ne domin ganin dan Kudu ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Masu Alaƙa