Gobara Ta Kashe Mutum 20, Uwa Da Ɗan Ta, Tumakai 20 Da Rumbun Hatsi 8 Suka Kone A Kano

Wata gobara da ta tashi da daddare ta yi ajalin mutane sama da 20 a garin Sheka da ke jihar Kano, kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito.
An ce ta kona wadanda abin ya rutsa da su har ba a iya gane su.
Haka zalika, yankin karamar Kano ya shiga cikin makoki yayin da wata gobarar dare ta kashe wata uwa mai shekaru 35, tare da jaririn ta mai shekaru uku a lokacin da suke barci.
Gobarar ta afku a Gandun Albasa-Bala Barodo da ke karamar hukumar Kano.
Gobarar ta afku a Gandun Albasa-Bala Barodo da ke karamar hukumar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusif Abdullahi.
Yace sun samu kiran gaggawa daga wani Ibrahim Ashiru cewa gini mai daki biyar ya kone gaba daya.
Saminu yace an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a sume kuma aka mika su ga Sufeto Shehu Lawan na ofishin yan sanda na Kwali, ya kara da cewa likitocin da ke bakin aiki a asibitin kwararru na Murtala Muhammad sun tabbatar da rasuwar su.
Gobarar ta kone fiye da mutane ashirin a wata gobara da ta tashi a daren ranar Alhamis a Sheka Karshen Kwalta.
Ya kara da cewa an kuma kona tumaki ashirin da silin hatsi takwas kurmus a karamar hukumar Kunchi.